An samu sabani a game da 2019 tsakanin Gwamna Dickson da Gboribiogha John-Jonah

An samu sabani a game da 2019 tsakanin Gwamna Dickson da Gboribiogha John-Jonah

Yayin da a ke shirin yin zaben fitar da gwani na gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa, mun samu labari cewa an fara samun matsala tsakanin gwamna mai barin-gado Seriake Dickson da mataimakinsa.

Kamar yadda mu ke samun labari daga Daily Trust, mataimakin gwamnan na Bayelsa watau Rear Admiral Gboribiogha John-Jonah ya ji haushin yadda mai gidansa ya zakulo wadanda ya ke so su gaje sa a 2019.

Seriake Dickson wanda ya ke shirin barin mulki ya zabi wasu daga cikin mutanensa uku ne da za su tsaya takarar gwamna a PDP. Wannan abu sam bai yi wa John-Jonah wanda gwamana bai tuntube sa dadi ba.

Da farko mataimkin gwamnan bai nuna sha’awar tsayawa takara a 2019 ba, sai dai yanzu Gboribiogha John-Jonah ya ruga ya yanki tikitin PDP. Hakan na zuwa ne bayan ya ga an yi wurgi da shi a lissafin 2019.

KU KARANTA: PDP ta na iya shan kashi a hannun APC a zaben Bayelsa - Jonathan

Gwamnan jihar na Bayelsa ya nuna cewa zai marawa daya daga cikin manyan na-kusa da shi baya ne a zaben tsaida gwanin da za a yi. ‘Yan takaran na sa su ne: Kemela Okara, Talford Ongolo, da kuma Douye Diri.

Dickson ya fito ya na cewa babu wanda ya isa ya samu tuta a PDP sai wadanda ke cikin tafiyarsa. Gwamnan ya nuna cewa babu wani mai neman tikitin PDP da zai iya kai labari a zaben na 2019 sai wanda ya ke so.

Babban gwamnan wanda ya ke shirin kammala wa’adinsa ya yi wannan jawabi ne a karshen makon jiya wajen kaddamar da ‘yan takarar jam’iyyar PDP na zaben shugabannin kananan hukumomi da za ayi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel