Mata sun koma yiwa maza fyade: An kwaci wani mutumi dakyar a hannun wata mata da take kokarin yi masa fyade

Mata sun koma yiwa maza fyade: An kwaci wani mutumi dakyar a hannun wata mata da take kokarin yi masa fyade

- Wani bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta na zamani ya bayyana yadda wani mutumi yake barka ihu yana neman taimako

- Mutumin yana ihun ne a yayin da wata mata ta ture shi kasa take kokarin cire masa gajeren wando

- Daga baya dai an zo an shiga tsakaninsu inda aka raba mutumin da matar wacce take kokarin yi masa fyade

A wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta ya bayyana yadda wata mata ta ture wani mutumi kasa take kokarin cire masa wanda, inda shi kuma mutumin ya barke da ihu yana neman taimako.

Daga baya kuma an hango wani mutumi yana gudu domin yaje ya shiga tsakanin abinda ke shirin faruwa tsakanin mutumin da matar wacce take sanye da gajeren wando, inda daga karshe ya kwaci mutumin dakyar.

KU KARANTA: Gayu mutanen Allah: Hotunan yadda 'yan sanda suka dinga yiwa gayu askin dole da almakashi a jihar Neja

Ba kasafai aka fiya samun mata sun yiwa maza fyade ba, kusan ko da yaushe sai dai kaji an ce namiji, amma kuma wasu lokutan wasu mazan da suke haduwa da matan da suka fi karfinsu, sun bayyana cewa lokuta da dama matan sukan yiwa maza fyade.

Misali a kasar Ghana, dokar kasar ba ta yadda da cewa mace tana iya yiwa namiji fyade ba, saboda haka ko mutum ya kai karar cewa mace tayi masa fyade ma yana batawa kansa lokaci ne, in ji wasu lauyoyi na kasa.

Amma idan har wannan bidiyon ya zamanto gaskiya, hakan yana nufin cewa da gaske ne mata na yiwa maza fyade.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel