Tsaro: 'Yan sanda sun kama masu laifi 79, sun kwato shanu 439 a Kaduna

Tsaro: 'Yan sanda sun kama masu laifi 79, sun kwato shanu 439 a Kaduna

Rundunar 'Yan sandan Najeriya reshen Jihar Kaduna, a ranar Laraba ta ce jami'an ta sun kama a kalla mutane 79 da ake zargi masu laifi ne tare da kwato shanu 439 a jihar cikin watan Yuli.

Kwamishinan rundunar na jihar, Ali Janga ne ya bayyana hakan yayin wata taron manema labarai a garin Rijana da ke karamar hukumar Kachia na jihar.

Ya ce, "Jaruman jami'an mu na SARS, AKU, IRT da sauran sassa sun samu nasara sosai yayin da suka kamo wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban har su 79."

Mr Janga ya ce ana zargin wadanda aka kama da aikata laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu, kisar gilla, sata, yin sojan gona da sayan kayan sata.

DUBA WANNAN: 2019: APC za ta iya lallasa PDP a zaben gwamnan Bayelsa - Goodluck Jonathan

"Ina son sanar da al'umma cewa muna bita kan samar da tsaro a titunan Kaduna-Abuja da Kaduna-Zaria da Kaduna-Birnin Gwari domin inganta tsaro a hanyoyin," inji shi.

Ya lissafa abubuwa da yawa da aka kwato hannun wadanda ake zargin da suka hada da bindigun kirar AK47 guda tara, bindigun farauta 3, albursai 954, wuka da zarto da sauransu.

Sauran abubuwan da suka kama sun hada da kudi N30,000, wayoyin salula, abin rufe fuska, takalma, shadoji da hulluna, mota kirar KIA Serato, Toyota Corolla, Marsandi da adaidaita sahu.

Sun kuma kwato shanu 439, tumaki 18, jakuna 8, babura 6, talabijin, komfuta, janerata da adduna.

Mr Janga ya kuma jinjinawa kokarin 'Yan sandan wurin gudanar da ayyukansu cikin ka'ida ciki har da wadanda suka warware zanga-zangar kungiyar IMN.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel