Gayu mutanen Allah: Hotunan yadda 'yan sanda suka dinga yiwa gayu askin dole da almakashi a jihar Neja

Gayu mutanen Allah: Hotunan yadda 'yan sanda suka dinga yiwa gayu askin dole da almakashi a jihar Neja

- Wasu jami'an hukumar 'yan sanda sun tare mutane da yawa a garin Kontagora dake jihar Neja suna yi musu askin dole da almakashi

- An bayyana cewa yawancin mutanen da 'yan sandan suke yiwa askin 'yan acaba ne wadanda suka yi askin da bai kamata ba

- Sai dai amma wannan lamari ya jawo kace-nace a cikin jama'a inda wasu ke ganin 'yan sanda basu da ikon yiwa mutane aski dan sun bar gashi kansu

Wasu jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya suna yiwa gayu askin dole da almakashi a garin Kontagora dake jihar Neja.

A rahoton da muka samu mutanen da 'yan sandan suke yiwa askin yawanci 'yan acaba ne wadanda suke yin askin da bai kamata ba.

Gayu mutanen Allah: Hotunan yadda 'yan sanda suka dinga yiwa gayu askin dole da almakashi a jihar Neja

Shave
Source: Facebook

Jami'an 'yan sandan sun nemo almakashi inda suke tare masu irin wannan aski suna aske musu shi da almakashin.

KU KARANTA: Cikin sauki zaka samu bindiga a Amurka, amma idan VISA ce sai kayi da gaske - Rihanna ta caccaki Donald Trump

Gayu mutanen Allah: Hotunan yadda 'yan sanda suka dinga yiwa gayu askin dole da almakashi a jihar Neja

Shave
Source: Facebook

Sai dai kuma wannan lamari ya jawo kace-nace a wajen jama'a inda wasu ke ganin 'yan sanda basu da ikon askewa mutane gashi dan sunyi askin da bai dace ba.

Barin gashi da yin aski wanda bai kamata ba ya zama ruwan dare a wajen matasa a wannan zamani, inda wasu ke ganin idan baka bar gashi ko kayi askin gayu ba mutum bai waye ba.

Gayu mutanen Allah: Hotunan yadda 'yan sanda suka dinga yiwa gayu askin dole da almakashi a jihar Neja

Shave
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel