Cikin sauki zaka samu bindiga a Amurka, amma idan VISA ce sai kayi da gaske - Rihanna ta caccaki Donald Trump

Cikin sauki zaka samu bindiga a Amurka, amma idan VISA ce sai kayi da gaske - Rihanna ta caccaki Donald Trump

- Fitacciyar mawakiyar kasar Amurka Rihanna ta caccaki shugaban kasar Amurka Donald Trump

- Mawakiyar ta caccaki shugaban kasar ne akan maganar da yayi ta kisan mutane 29 da aka yi a kasar

- Rihanna ta bayyana cewa ba ta san wacce irin kasa bace da siyan bindiga yake da sauki ba fiye da samun VISA

Fitacciyar mawakiyar kasar Amurka Rihanna ta caccaki shugaban kasar Amurka Donald Trump, bayan yayi magana akan mutane 29 da aka kashe a kasar.

Bayan harbe-harben da aka yi a El Paso, Texas wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 20, shugaba Trump yayi magana a shafinsa na Twitter kamar haka, "Harbe-harben da aka yi yau a Texas bai yi mana dadi ba ko kadan, kuma ta'addanci ne. Na san ba ni daya bane nake jimamin wannan abu da ya faru a kasar nan. Babu wani dalili da zai sa a dinga kashe mutane basu ji ba basu gani ba."

Wannan magana da shugaban kasar yayi ita ce ta sanya mai da masa da martani, inda ta ce, "Um...Donald baka iya rubuta sunan ta'addanci daidai ba! Kasarka ta samu hari na 'yan ta'adda har sau biyu a lokaci daya inda yayi sanadiyyar mutuwar kusan mutane 30.

KU KARANTA: Allah ya kyauta: Wani mutumi ya kashe surikansa da dansa sannan ya kashe kanshi, saboda matarsa ta nemi ya saketa

"Wannan abu bai yi dadi ba, kwanaki kadan bayan harin da aka kai birnin California, inda 'yan ta'adda suke da damar siyan bindiga babu doka a birnin Vegas, sannan suka nufi wurin sayar da abinci suka kashe mutane 6 ciki hadda jariri!

"Wacce irin duniya ce wannan da siyan bindiga yake da sauki fiye da samun VISA!

"Wacce irin kasa ce da za ayi gini kawai domin a dinga ajiye 'yan ta'adda cikinta. Ina mika sakon ta'aziyya ta ga iyalan mutanen da aka kashe na kasar Texas, California da Ohio."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel