Allah ya kyauta: Wani mutumi ya kashe surikansa da dansa sannan ya kashe kanshi, saboda matarsa ta nemi ya saketa

Allah ya kyauta: Wani mutumi ya kashe surikansa da dansa sannan ya kashe kanshi, saboda matarsa ta nemi ya saketa

- Wani mutumi ya kashe surukansa, dansa da kansa a kasar Amurka bayan wata shawara da matarsa ta yanke

- Matar tasa ta yanke shawarar rabuwa da shi, inda ta nemi ya saketa

- Wannan lamari bai yiwa mutumin dadi ba, inda ya dauki bindiga ya nufi gidansu matar ya budewa iyayenta wuta tare da danshi

Wani mai amfani da shafin sada zumunta na Twitter mai suna Jamal Nathaniel ya wallafa wani labari na yadda wani dan uwansa ya kashe surikansa da dansa na cikinsa sannan kuma daga baya ya kashe kanshi, duka saboda matarsa ta nemi ya saketa.

Hukumomin tsaro na kasar Amurka sun bayyana cewa mutanen da mutumin ya kashe sun hada da Vickie Danita mai shekaru 54 da Gregory Bruce Pickeral mai shekaru 53 da kuma Mark Mckinley Hughes Jr. mai shekaru 42 a duniya.

Wannan lamari dai ya faru ne a Charles County dake garin Maryland, cikin kasar Amurka a ranar 2 ga watan Agusta. Kakakin rundunar 'yan sandan yankin Diane Richardson, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa an garzaya da dan gidan mutumin da yayi harbin mai shekaru 11.

KU KARANTA: Muna zinace-zinace da shan kwayoyi da sunan jihadi - Tubabben Boko Haram

Bincike ya nuna cewa Hughes ya shiga gidan surukan nashi ne kawai ya bude musu wuta. Bayan ya gama kashe surukan nashi, sai ga wata mota ta tsaya a kofar gidan, ashe dan shine a cikin motar da 'yar uwarshi ta dauko za ta kawo shi gidan kakannin ya wuni.

Da zuwan motar Hughes ya fara harbinta, inda har ya samu dan nashi, matar da ke cikin motar bata mutu ba amma ta ji munanan raunika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel