Rundunar 'yan sanda ta yi kashed da babbar murya ga 'yan 'Adaidaitasahu' a jihar Kano

Rundunar 'yan sanda ta yi kashed da babbar murya ga 'yan 'Adaidaitasahu' a jihar Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi kashedi da babbar murya ga direbobin babur mai kafa uku, wadanda aka fi kira da 'Yan-adaidaita sahu, da su guji haddasa hatsari da aikata saura laifuka a kan manya da kananan titunan da ke birnin Kano.

Rundunar 'yan sandan ta ce zata fara daukan tsatsauran mataki daga yanzu a kan direbobi da fasinjojin Adaidaita sahu.

A wani jawabi da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya fitar ranar Talata, rundunar 'yan sandan ta ce dole kowanne dan sahu daga yanzu ya mallaki lambar rijista da hukumar KAROTA tare da makala lambar a jikin babur dinsa.

Rundunar ta bayyana cewa duk direban sahun da aka kama yana daukan fasinja a gefensa ko kuma bashi da lambar rijista da hukumar KAROTA, za a kama shi a kuma gurfanar da shi a gaban kotu.

DUBA WANNAN: Abu 5 da ya kamata ku sani a kan asibitin da za a kai Zakzaky a kasar Indiya

Jawabin ya kara da cewa, rundunar 'yan sanda zata yi hakan ne domin tsare lafiya da dukiyoyin mutanen jihar Kano.

"Muna kira ga jama'a da su daina shiga adaidaita sahun da suka ga direba ya dauko fasinjoji fiye da ka'ida ko kuma babura marasa lamabar rijista da hukumar KAROTA," a cewar jawabin.

Masu motoci da sauran ababen hawa na yawan korafi da halayyar wasu direbobin adaidaita ta ganganci a kan titi da kuma karya dokokin tuki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel