Daga karshe: An fitar da jadawalin rantsar da sabbin ministocin Buhari

Daga karshe: An fitar da jadawalin rantsar da sabbin ministocin Buhari

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta hannun ofishin babban sakatarenta, ta fitar da jadawalin shirye-shiryen rantsar da sabbin zababbun ministocin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sakatare a ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya, Babatunde Lawal, ya bayyana cewa za ayi ganawa ta musamman da sabbin ministocin domin zantawa akan sanin makaman aiki a ranakun 19 da 20 ga watan Agusta.

Sannan kuma a ranar 21 ga watan Agusta, za a hallara gaba daya a fadar shugaban kasa inda za a rantasar sabbin ministocin sannan kowa ya san ma’aikatar da zai yi aiki.

Cikin wadanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sun hada da tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom Godswill Akpabio, Babban Lauya Festus Keyamo, tsohon gwamnan jihar Benuwai George Akume da wasu mutane guda 40.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta ba da umurnin daskarar da asusun gwamnatin jihar Lagas kan zargin zambar N9.9b

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta bayyana kudurinta na gina sabbin dakunan gwaje-gwajen kimiyya a jami’o’i shida dake bangarori daban-daban na kasar nan.

Babban sakatare a ma’aikatar kimiyya da kere-kere ta tarayya, Mista Bitrus Nabasu ne ya bada wannan sanarwa, inda ya ce gwamnati na da burin ganin Najeriya ta shiga sahun kasashe 20 masu mafi kyawon tattalin arziki a duniya nan bada jimawa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel