2019: APC za ta iya lallasa PDP a zaben gwamnan Bayelsa - Goodluck Jonathan

2019: APC za ta iya lallasa PDP a zaben gwamnan Bayelsa - Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan ya ce idan ba a samu hadin kai a jam'iyyar reshen jihar Bayelsa ba akwai yiwuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta kayar da PDP a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a Nuwamban 2019.

Mai bayar da shawara na musamman na Gwamna Seriake Dickson kan kafafen watsa labarai, Mr Fidelis Soriwei ne ya ce ya jiyo tsohon shugaban kasar ya fadi hakan yayin taron kwamitin datttawan PDP da aka yi a gida gwamnati da ke Yenagoa a ranar Talata.

Jonathan ya ce: "Hadin kai ne kawai za iya bamu nasara amma idan bamu hada kan mu ba toh APC za su iya lashe zaben.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: PDP ta dakatar da shugabaninta 5 da wasu mutane 9 a Kebbi

"Misali, Hadin kan mutanen Rivers maza da mata ne da suka ki amincewa sojoji suyi abinda su ke so ne ya sa PDP tayi nasara a jihar. Ba don hakan ya faru ba da jam'iyyar adawa tayi nasara a jihar.

"Duk da cewa APC a Bayelsa ba ta da karfi a matakin mazabu, kananan hukumomi da jihar za ta iya lashe zaben gwamna ta ranar 16 ga watan Nuwamban 2019, ya zama dole PDP ta hada kai domin yin nasara a jihar.

"Ina rokon dukkan 'yan takara su dena ci wa juna mutunci. Dole mu mutunta juna domin daga karshe zaya daga cikin ku ne zai zama dan takara kuma dole sauran za suyi aiki tare da shi.

"Idan muna son PDP tayi nasara a jihar nan, muna bukatar hadin kai sosai shi yasa dole 'yan takara 21 su hada kansu tunda a karshe za mu yi wa duk wanda ya zama dan takarar aiki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel