Toh fah: An damke masu zanga-zangar juyin juya hali 56

Toh fah: An damke masu zanga-zangar juyin juya hali 56

Rahotanni sun kawo cewa an kama akalla mutane 56 a wajen zanga-zangar juyin juya hali da aka gudanar a fadin kasar. Wani lauya mai kare hakkin al’umma, Inibene Effiong ne ya bayyana hakan.

Effiong wanda ya kasance lauyan da ke kare jagoran zanga-zangar da ke tsare, wato Omoyele Sowore, ya bayyana tsare wannan adadin ne a shafin sa na Facebook a jiya Litinin, 5 ga watan Agusta da tsakar dare.

An dai kama Sowore tuntsakar daren ranar Asabar, kwana biyu kafin lokacin yin zanga-zangar ta juyin juya hali da aka sirya gudanarwa a fadin kasar.

Effiong ya karyata zargin da gwamnatin tarayya ta yi cewa an shirya zanga-zanagar ce da nufin a kifar da gwamnatin Buhari.

Daga cikin ‘yan jarida da aka kama har da Ibrahim Danhalilu, tsohon editan labaran siyasa na jaridar Daily Trust.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe wani malamin addini sannan suka yi garkuwa da matarsa a Kaduna

Sai dai shi Danhalilu an kama shi ne sakamakon wani rubutu da ya yi a shafin sa na Facebook, inda ya nuna goyon bayan a yi zanga-zangar.

Daga cikin jihohin da aka kama masu zanga-zanga akwai Lagos, Cross River, Ondo da kuma Ogun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel