Kotu ta ba da umurnin daskarar da asusun gwamnatin jihar Lagas kan zargin zambar N9.9b

Kotu ta ba da umurnin daskarar da asusun gwamnatin jihar Lagas kan zargin zambar N9.9b

Biyo bayan zargin zambar naira biliyan 9.9, babbar kotun tarayya a jihar Lagas, karkashin jagorancin Justis Chuka Obiozor, a ranar Talata, 6 ga watan Agusta, tayi umurnin daskarar da asusun banki guda uku mallakar gwamnatin jihar Lagas.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta gabatar da zargin a wani kara da ta shigar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Justis Obiozor yayi umurnin daskarar da asusun uku a sabbin bankuna, har sai an kammala bincike da zartar da hukunci akan Adewale Adesanya, sakataren din-din-din na ofishin Shugaban ma’aikatan gwamna.

Kungmi Daniel, wani mai bincike na EFCC, ya bayyana cewa hukumar ta gano makudan kudade na N9,927,714,443.29 da suka fita daga baitul malin jihar zuwa daya daga cikin asusun da ake Magana a kai, wanda yake mallakar Adesanya sannan an ude asusun ne a watan Satumba, 2018 lokacin gwamnatin Akinwunmi Ambode.

KU KARANTA KUMA: Karin bayani: Kotu ta tsayar da ranar za ta zartar da hukuncin kan bukatar FG na tsare Sowore na kwananki 90

Justis Obiozor ya amsa rokon hukumar yaki da rashawar sannan ya dage zaman zuwa ranar Juma’a, 9 ga watan Agusta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel