Karin bayani: Kotu ta tsayar da ranar za ta zartar da hukuncin kan bukatar FG na tsare Sowore na kwananki 90

Karin bayani: Kotu ta tsayar da ranar za ta zartar da hukuncin kan bukatar FG na tsare Sowore na kwananki 90

Wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsayar da ranar Alhamis 8 ga watan Augusta domin zartar da hukunci kan bukatar gwamnatin tarayya na neman izinin tsare shugaban RevolutionNow, Omoyele Sowore.

Jami'an Hukumar 'Yan sandan farar kaya na DSS ne suka damke tsohon dan takarar shugaban kasar a dakin Otel din sa da ke Legas a daren Juma'a kuma suke tsare da shi har yanzu duk da cewa wasu na ta kiraye-kirayen a sake shi.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta zargi Sowore da aikata cin amanar kasa yayin da ya yi kira da 'yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwata a tittunan kasar a ranar 5 ga watan Augusta domin nuna rashin jin dadinsu kan rashin kulawa da halin da 'yan Najeriya ke ciki da gwamntin keyi.

DUBA WANNAN: An bindige shugaban wata kungiyar 'yan kasuwa a Zakibiam

Wasu daga cikin wadanda suka fita yin zanga-zangar sun yi artabu da jami'an tsaro duba da cewa Rundunar 'Yan sanda ta haramta yin zanga-zangar tun kafin a fara yin sa.

A takardar da ta shigarwa kotu a ranar Talata, Gwamnatin Tarayya (FG) ta hannun DSS ta nemi kotun ta bata kwanaki 90 domin kammala bincike kan ayyukan ta'addanci da ta ke zargin Sowore da aikatawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel