Abu 5 da ya kamata ku sani a kan asibitin da za a kai Zakzaky a kasar Indiya

Abu 5 da ya kamata ku sani a kan asibitin da za a kai Zakzaky a kasar Indiya

A ranar litinin, 05 ga watan Agusta, ne wata babbar kotun jihar Kaduna ta bayar da belin shugaba 'yaan Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, domin ya fita kasar Indiya a duba lafiyarsa, kamar yadda lauyoyinsa suka bukata.

Kotun ta gindaya sharadin cewa jami'an tsaron gwamnatin Najeriya ne zasu raka Zakzaky zuwa asibitin na kasar Indiya domin su tiso keyarsa ya dawo Najeriya da zarar ya warke.

Ga wasu abubuwa biyar da ya kamata 'yan Najeriya su sani dangane da asibitin da za a kai Zakzaky da matarsa, Zeenat, a kasar Indiya.

1. Sunan asibitin 'Medanta' kuma yana garin Lucknow a jihar Uttar Pradesh ta kasar Indiya.

2. Asibiti ne na musamman da ke duba masu larurar Koda da ciwon Zuciya. Duka da ba a bayyana takamaiman cutar da ke damun Zakzaky ba, magoya bayansa sun ce lafiyarsa tana cikin tsaka wuya.

DUBA WANNAN: Kacibus: An kama gawurtaccen dan fashi da ake nema ruwa a jallo a wani asibitin Katsina

3. Asibitin ya yi suna wajen magance cututtuka ta hanyar amfani da kimiyyar zamani da ba kowanne asibiti ke da irinta ba. Hakan ne ma yasa aka zabi asibitin a matsayin wanda za a kai Zakzaky, saboda asibitin ba ya kwantar da mutum ya wuce kana 7.

4. Asibitin na daya daga cikin manyan asibitoc a yankin Uttar Pradesh, yana da gado 1250 na kwantar da marasa lafiya.

5. Yana daya daga cikin asibitocin duniya da ke iya amfani da wata fasahar zamani wajen duba marar lafiya daga ko ina yake a fadin duniya (telemedicine programme). Ana tunanin asibitin zai yi amfani da irin wannan fasaha a kan Zakzaky kafin a fitar da shi zuwa ksar Indiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel