Kacibus: An kama gawurtaccen dan fashi da ake nema ruwa a jallo a wani asibitin Katsina

Kacibus: An kama gawurtaccen dan fashi da ake nema ruwa a jallo a wani asibitin Katsina

An kama wani mutum, Haruna Maiyara, mai shekaru 35, a babban asibitin jihar Katsina inda da yake karbar magani sakamakon harbinsa da bindiga.

Jami'an 'yan sanda sun kama Maiyara, mazaunin unguwar Budawa a karamar hukumar Safana a jihar Katsina, bisa zarginsa da aikata laifin fashi da makami, wanda ta sanadin hakan ne ya samu ciwon da ya kwantar a asibiti.

Majiyar mu ta bayyana cewa jami'an 'yan sanda sun samu nasarar gano Maiyara ne ta hanyar samun bayanan sirri daga 'Yansakai dake yankin da babban asibitin Katsina ya ke.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa Maiyara da ragowar yaransa, da ake nema ruwa a jallo, sun kashe manoma uku a gonakinsu a wani hari da suka kai kauyen Kirkawa da ke karamar hukumar Safana a ranar 8 ga watan Yuni, 2019.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Zamfara za ta fara biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi

Manoman da suka kashe sune; Jabiru Mansir, Ashiru Mansir da Mundaha Mansir.

Tuni rundunar 'yan sanda ta gurfanar da Maiyara a gaban kotu bisa tuhumarsa da aikata laifukan da suka hada da hada baki domin aikata laifi, kisan kai da sata da sauransu.

Ana sa ran za a gabatar da Maiyara a gaban babbar kotun majistare da Hajiya Fadile Dikko ke jagoranta a ranar 15 ga watan Agusta, 2019.

Tuni kotun ta bayar da umarnin a cigaba da tsare shi a gidan yari har zuwa ranar da za a gabatar da shi a gabanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel