Eid-el-Kabir: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da Litinin da Talata a matsayin ranakun hutu

Eid-el-Kabir: Gwamnatin tarayya ta kaddamar da Litinin da Talata a matsayin ranakun hutu

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranakun 12 ga watan Agusta da 13 ga watan Agusta a matsayin hutu domin yin bikin babbar sallar 2019.

Mohammed Manga, daraktan labarai, na ma’aikatar cikin gida a wani jawabi da ya saki a ranar Talata, 6 ga watan Agusta a Abuja, yace sakatariyar din-din-din na ma’aikatar, Georgina Ehuriah, ce ta kaddamar da hakan.

Ehuriah ta taya al’umman Musulmi murnar wannan biki, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito.

Ta yi kira ga dukkan yan Najeriya da su yi amfani da bikin wannan shekarar wajen wanzar da aminci, kauna da kuma zaman lafiya kamar yadda fiyayyen hallita annabi Mohammed ya koyar.

Ta bukaci yan Najeriya da su guje ma duk wani rikici sannan su hadu tare da gwamnatin tarayya wajen gina zaman lafiya, da kuma hadin kan kasar.

KU KARANTA KUMA: Afuwa: Gwamnan Zamfara ya sallami fulanin daji 100 daga dauri

Ehuriah ta sake jadadda jajircewar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya.

A wani labarin kuma mun ji cewa hukumar tabbatar da jin dadin Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta kammala jigilar manniyatan Najeriya 44,450 zuwa kasa mai tsarki.

Wannan adadi ya hadar da ma'aikata da za su yi masu hidima daga dukkanin jihohin kasar da kuma garin Abuja.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayar da shaida, wannan adadi bai hadar da maniyyatan Najeriya ba wadanda suka dira a kasar Saudiya ta hanyar jirgin yawo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel