Gwamnatin tarayya za ta gina sabbin dakunan gwaje-gwajen kimiyya a Jami’o'i shida

Gwamnatin tarayya za ta gina sabbin dakunan gwaje-gwajen kimiyya a Jami’o'i shida

-Gwamnatin Najeriya za ta gina sabbin dakunan gwaje-gwajen kimiyya na zamani a jami'o'i shida

-Babban sakatare a ma'aikatar kimiyya da kere-kere Mr Bitrus Nabasu ne ya bada wannan sanarwa ranar Talata

-Nan bada jimawa ba Najeriya za ta kasance cikin jerin kasashe 20 mafi karfin tattalin arziki a duniya a cewar sakataren

Gwamnatin tarayya ta bayyana kudurinta na gina sabbin dakunan gwaje-gwajen kimiyya a jami’o’i shida dake bangarori daban-daban na kasar nan.

Babban sakatare a ma’aikatar kimiyya da kere-kere ta tarayya, Mista Bitrus Nabasu ne ya bada wannan sanarwa, inda ya ce gwamnati na da burin ganin Najeriya ta shiga sahun kasashe 20 masu mafi kyawon tattalin arziki a duniya nan bada jimawa ba.

KU KARANTA:Shugaba Buhari zai rantsar da ministoci ranar 21 ga watan Agusta

Nabasu ya fadi wannan maganar tasa ne a ranar Talata lokacin da yake karbar wata lambar girma daga hannun Kungiyar Daliban Najeriya wato NANS.

Sakataren ya ce: “ Gwamnatin tarayya za ta gina dakunan gwaje-gwajen kimiyya a jami’o’i shida dake kasar nan. Ko wane bangare zai kasance yana da guda daya.”

Haka zalika, Sakataren ya shaidawa kungiyar daliban cewa, gwamnatin tarayya na daf da kaddamar da sabuwar dokar Executive Order 5 wadda za ta mayar da Najeriya kasa mai dogaro ga ilimi a matsayin hanyar tattalin arziki zuwa shekarar 2030.

Ya kara da cewa: “ Nan bada jimawa ba Najeriya za ta kasance cikin jerin kasashe 20 da suka fi kowa karfin tattalin arziki a fadin duniyar nan.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel