NBC ta bawa Jami'ar Bayero lasisin bude gidan talabijin

NBC ta bawa Jami'ar Bayero lasisin bude gidan talabijin

Hukumar da ke kula da gidajen Talabijin da Rediyo ta Najeriya, NBC, ta bawa Jami'ar Bayero da ke Kano, BUK lasisin fara watsa shirye-shirye na talabijin.

Shugaaban NBC, Ishaq Kawu na ya bayyana hakan a ranar Talata inda ya ce bayar da lasisin zai bawa jami'ar daman kafa gidan talabijin din ta da kuma horas da dalibai a fanin watsa shirye-shirye a talabijin.

"Hukumar mu tana da kyakyawan alaka da jami'ar ta fannin yada labarai" kamar yadda aka ruwaito Mr Kawu ya fadi a shafinsa na Facebook.

DUBA WANNAN: Ganduje vs Abba Gida-Gida: PDP ce ta nemi a yi zaben kece raini - Yakasai

Kawu ya bayyana hakan ne yayin da ya tarbi tawagar mahukunta jami'ar a ofishinsa a ofishinsa.

Jami'ar tana da gidan rediyo da ke watsa shirye-shirye ga daliban jami'ar da unguwannin da ke makwabtaka da ita.

A bangarensa, shugaban jami'ar, Muhammad Bello ya bayyana godiyarsa ga Mr Kawu da hukumar ta NBC bisa bawa jami'arsa lasisin.

Ya yi alkawarin cewa jami'ar za tayi amfani da lasisin ta hanyar da ya da ce "bisa tsarin dokokin da Hukumar da gidajen Talabijin da Rediyo na kasa ta shimfida da kuma bayar da gudunmawa ga fanin yadda labarai da cigaban kasa."

Mr Bello ya ce lasisin ya zo a lokacin da ya dace duba da cewa tsagayar koyar aikin jaridar tana fadada ayyukan ta a yanzu.

Ya ce za ayi amfani da lasisin wurin bawa dalibai horo kan aikin jarida na binciken kwakwaf tare da basu damar aiwatar da abubuwan da ake koyar da su a ajujuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel