An bindige shugaban wata kungiyar 'yan kasuwa a Zakibiam

An bindige shugaban wata kungiyar 'yan kasuwa a Zakibiam

Hankula sun tashi a garin Zakibiam bayan kisar gillar da aka yiwa shugaban kungiyar masu rumfuna a Kasuwar Doya na garin, Mr Tavershima Achinge a karamar hukumar Ukum na jihar Benue.

Wasu da ake zargin 'yan daban garin ne suka kashe Achinge a ranar Litinin.

Wani shaidan ganin ido mai suna Toryila Aye ya shaidawa The Nation cewa marigayin ya koma gidansa a Zakibiam ne bayan ya gama cin kasuwar Doya ta Zakibiam wacce ke daya daga cikin manyan kasuwannin doya a kasar.

An ce 'yan bindigan sun kai farmaki gidansa ne suka harbe shi da bindiga a kirjinsa ta yadda ba zai yi rai ba.

DUBA WANNAN: An bi wani magidanci har gidansa an harbe shi a Katsina

Binciken da majiyar Legit.ng tayi ya nuna cewa kisar ba zai rasa nasaba da yunkurin da wasu ke yi na ganin an basu kwangilar samar da tsaro a kasuwar ba.

Majiyar ta gano cewa wani shugaban kungiyar 'yan daba a garin ya dade yana tursasa wa marigayin ya sakar masa kwangilar samar da tsaro a kasuwar ta doya amma marigayin ya ce masu shagunan za su cigaba da tsare kayansu domin a baya da aka bawa wasu gadin anyi asarar doya na daruruwan naira.

A halin yanzu dai an rufe kasuwar doyar da Zakibiam saboda tsoron harin ramuwar gayya yayin da 'yan kasuwa da su kayi tafiya daga wurare masu nisa kuma sun shiga mayuyacin halin.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, DSP Kate Aneene Sewuese ya tabbatar da kisar kuma ya ce a halin yanzu rundunar ta 'yan sanda ta fara bincike domin gano wadanda suka aikata mummunan aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel