Yanzu Yanzu: Yan fashi da makami sun kai hari banki a Ondo

Yanzu Yanzu: Yan fashi da makami sun kai hari banki a Ondo

Wasu yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun kai hari wani tsohon banki da ke Iju-Itaogbolu a yankin Akure ta arewa na jihar Ondo.

Sahara Reporters ta kawo cewa yan fashin kumanin su shida, sun kai mamaya bankin a ranar Talata sannan suka fara har ba kakkautawa.

Yan bindigan sun ji ma ma’aikatan ankin da dama sun ji rauni.

Lamarin ya shafi harda kwastamomi, da suka zo harkokinsu a cikin bankin.

Wata majiya, wacce ta tabbatar da labarin ga wakilinmu, ta bayyana cewa yan fashin sun shiga bankin ta karfin tuwo sannan suka tsere da makudan kudade.

Majiyar ta bayyana cewa jami’an tsaro sun yi musayar wuta da yan fashin.

“Yanzun nan suka kai hari banki a Iju-Itaogolu sannan kowa ya nemi mafaka domin tsiratar da rayuwarsa.

KU KARANTA KUMA: Sallah: Buhun shinkafa ya koma N18,000 yayinda farashin kayan abinci yayi tashin gauron zai a Lokoja

“Na ga mutane da dama dauke da rauni sannan ina sane da cewar yan fashin sun kashe wasu mutane da ba za a iya fadin ko su wanene ba a yanzu,” inji majiyar.

Kwamishinan yan sandan jihar Ondo, Unide Adie, ya tabbatar da harin a wani hira da Sahara Reporters.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel