Yan bindiga sun kashe wani malamin addini sannan suka yi garkuwa da matarsa a Kaduna

Yan bindiga sun kashe wani malamin addini sannan suka yi garkuwa da matarsa a Kaduna

Yan bindiga sun kashe wani fasto na cocin Living Faith, Jeremiah Omolara yayinda suka yi garkuwa da matarsa a yankin Agwan Romi da ke jihar Kaduna.

Koda dai an tattaro cewa lamarin ya afku ne a ranar Lahadi, a hanyar Kaduna zuwa Abuja, cikakken bayani lamarin ya billo ne a ranar Litinin, 5 ga watan Agusta.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, Yakubu Sabo bai yi sharhi ba akan lamarin a daidai lokacin kawo wannan labari.

An tattaro cewa yan bindigan sun bude wuta a kan motarsu, inda suka kashe faston a nan take yayinda suka tafi da matarsa zuwa daji, Joseph Hayab, shugaban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar ya tabbatar da lamarin.

KU KARANTA KUMA: Sallah: Buhun shinkafa ya koma N18,000 yayinda farashin kayan abinci yayi tashin gauron zai a Lokoja

Hayab ya koka kan yawan garkuwa da mutane a Kaduna, musamman sace malaman addini.

Yace kisan faston da garkuwa da matarsa ya kasance abun bakin ciki.

A wani labarin kuma, mun ji cewa a yayin ci gaba da zage dantse wajen tabbatar da sulhu, gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle, ya kudiri aniyar yin afuwa tare da gafarta wa fursunonin 'yan banga da kuma fulani dake tsare a gidajen cin sarka.

Cikin wata sanarwa da ta fito daga harshen mai magana da yawun gwamnan jihar, Zailani Bappah, ya ce ababen zargin wadanda ke da hannun cikin annobar ta'addanci da ta yiwa jihar daurin kama-karya za su samu 'yanci a wannan mako.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel