Shugaba Buhari zai rantsar da ministoci ranar 21 ga watan Agusta

Shugaba Buhari zai rantsar da ministoci ranar 21 ga watan Agusta

Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin tarayya wato SGF ne ya bada wannan sanarwa ga gidan talbijin na ChannelsTv cewa Shugaban kasa zai rantsar da ministoci ranar Laraba 21 ga watan Agusta, 2019.

KU KARANTA:Hatsarin babbar mota ya kashe mutum 2 a Binuwe

Zancen rantsar da ministocin ya fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha. A cikin zance sakataren ya fadi cewa za’a gudanar da bikin rantsar da ministocin ne da karfe 11 na safe a Fadar Shugaban kasa dake Abuja ranar 21 ga watan Agusta.

Har ila yau, zancen ya bayyana mana cewa za’a fara shirye-shiryen rantsar da ministocin tun daga ranar 19, inda ake sa ran dukkanin ma’aikatan dake aiki a karkashin ma’aikatun gwamnatin tarayya za su halarci taron.

Za’a gudanar da wannan taro na ranar 19 da 20 ga watan Agusta domin yin takaitaccen bayani ga sabbin ministocin saboda su fahimci yanayin aikin da suke shirin karba na ministoci.

Haka zalika, zancen ya rufe jawabinsa da cewa, a ranar karshe wadda ita ce Laraba 21 ga watan Agusta ne za a rantsar da ministocin ga baki dayansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel