Kungiyar IMN ta Zakzaky ba tsantsar ta Shi'a ba ce – Inji Sheikh Hamzah Lawal

Kungiyar IMN ta Zakzaky ba tsantsar ta Shi'a ba ce – Inji Sheikh Hamzah Lawal

Sheikh Hamzah Lawal wani tsohon Jigo ne a tafiyar kungiyar IMN a karkashin Ibrahim Zakzaky a baya, wanda yanzu ya fito ya barrantar da wannan babbar kungiya daga akidar Shi’anci.

Hamzah Lawal ya bayyana cewa babu wata alaka tsakanin addinin Shi’a da kuma kungiyar IMN ta Ibrahim Zakzaky. Lawal ya ce IMN tafiya ce ta juyin juya-hali, inda ita kuwa Shi'a akida ce.

Malamin ya ke cewa kungiyar Zakzaky ta fi kusa da tafiyar Sunnah a kan Shi’a wanda su ke kishiyantar juna. Malamin ya yi wannan bayani ne a wani jawabi da ya fitar cikin kwanakin nan.

Babban Shehin na Shi’a da ke Garin Kaduna shi ne Sakataren kungiyar nan ta Atthakalaini a Najeriya. Wannan kungiya ta na ikirarin cewa ita ce ke koyar da tsantar addinin Shi’a a kasar.

Sheikh Lawal wanda ya kurbi akidar Shi’a daga kasar Iran, kamar yadda jama’a da yawa su ka sani, ya na cikin tafiyar Zakzaky na tsawon shekaru 20 na farko, kafin ya bangare a shekarar 2000.

KU KARANTA: Tsohon 'Dan Boko Haram ya tona asirin abin da su ka yi a da

Malamin ya ce IMN ta tara Mabiya daga kungiyoyi da-dama a cakude cikin tafiyarsa ta siyasa wanda a cewarsa wannan ne babban abin da ya jawowa Ibrahim Zakzaky matsala da hukuma.

Ga kadan daga abin da wannan Bajimin Malami na Shi’a ya ke fada a game da tafiyar Zakzaky:

"Babu shakka Zakzaky ya rasa inda zai sa kan sa bayan da ya bar Sunnah ya kama akidar Shi'a, sai ya ci karo da matsaloli biyu; ko ya rike Mabiyansa na Sunnah, ko ya bi Shi’a yi watsi da su…”

Shehin Shi’ar ya cigaba da cewa: “Saboda son Duniya sai Zakzaky ya koma tafiya kan wani tafarki mai ruwa-biyu, shi ba ya cikin Shi’a kuma sannan bai shiga tafarkin Sunnah tsundum ba.”

A jawabin na Malamin addinin, ya nemi a saki Ibrahim Zakzaky, kuma ya ja kunnen irin su Iran da Saudiyya da su shiga taitayinsu, su daina kokarin dasa wutan rikici a Najeriya, su ji da kasashensu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel