Buhari ya jinjinawa yan Najeriya da suka kaurace ma zanga-zangar juyin hali

Buhari ya jinjinawa yan Najeriya da suka kaurace ma zanga-zangar juyin hali

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa daukacin al’umman Najeriya wadanda kaurace ma kiraye-kirayen da aka rika yi a shafukan sada zumunta akan su fito zanga-zangar juyin juya hali, inda suka mayar da hankali ga harkokin gabansu.

Babban hadimin Shugaban kasa a kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 5 ga watan Agusta cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja.

Ya ce shugaban kasar ya ji dadin goyon bayan da aka baiwa tafiyar dimokradiyya a Najeriya.

Har ila yau shugaban kasar ya bayyana cewa duk da akwai wadansu daruruwan mutane wadanda suka fita gangamin, sun yi akan ne a bisa cimma muradin kawukansu amma ba don manufar kasa ba.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zangar juyin juya hali: Sowore ya ce a ci gaba da gashi

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa jami’an tsaro sun karbe harabar ‘Freedom Park’ wajen da aka shirya gudanar da zanga zangar juyin juya hali da aka sake shiryawa a Ojota da ke jihar Legas.

‘Freedom Park’ wajen shakatawa da aka sanya ma sunan marigayi Gani Fawehinmi, ya kasance wajen da masu zanga zangar kwato ma al’umma hakki a jihar ke yawan gudanar da zanga-zangarsu.

Sai dai jaridar This Day ta rahoto cewa akwai rundunar soji a mashigin wajen shakatawan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel