Shugaban majalisar dattijai ya fitar da sabon hotonsa a hukumance da kuma lakabin da za ke kiransa da shi

Shugaban majalisar dattijai ya fitar da sabon hotonsa a hukumance da kuma lakabin da za ke kiransa da shi

Ofishin shugaban majalisar dattijai, Ahmda Lawan, ya fitar da hotonsa za a ake amfani da shi a hukumance da kuma lakabin da za ake hada wa tare da sunansa.

A wani sakon ta na'ura mai kwakwalwa da ofishin ya aike wa manyan kafafen yada labarai na kasa, an bayyana cewa, "tare da wannan sako akwai hoton mai girma shugaban majalisar dattijai da za ake amfani da shi a hukumance."

Sanna sakon ya cigaba da cewa, "shugaban majlisar dattijai ya zabi da ake kiransa da: Ahmad Ibrahim LAwan, Ph.D, CON, kamar yadda ya ke a jikin hoton."

Shugaban majalisar dattijai ya fitar da sabon hotonsa a hukumance da kuma lakabin da za ke kiransa da shi

Sabon hoton shugaban majalisar dattijai a hukumance da kuma lakabin da za ke kiransa da shi
Source: Facebook

A ranar Litinin, 05 ga watan Agusta, ne shugaban majalisar ta dattijai ya tashi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Cabdijam: Tsohon gwamnan APC ya fitar da biliyan N19.8 ana sauran awanni ya mika mulki - EFCC

Kazalika, shi ma gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya tashi zuwa kasar ta Saudiyya a ranar Talata, 06 ga watan Agusta, domin gudanar da aikin Hajji.

Da yake magana da manema labarai kafin tashinsa, gwamna Bello ya bayyana cewa wannan shine karo da zai halarci aikin Hajji tun bayan zamansa gwamna a shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel