Hatsarin babbar mota ya kashe mutum 2 a Binuwe

Hatsarin babbar mota ya kashe mutum 2 a Binuwe

-Wata babbar mota ta murkushe babur wanda yayi sanadiyar mutuwar mutanen dake samansa

-Hatsarin ya auku ne Makurdi babban birnin Binuwe da misalin karfe 8:40 na safiyar Talata

-Jami'in hulda hukumar kiyaye hadurra ta kasa wato EFCC a jihar Binuwe ne ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin ta hanyar hirar tarho da manema labarai

Wata babbar mota a safiyar Talata 6 ga watan Agusta, 2019 ta murkushe mutum biyu har lahira a kan titin Otukpo dake birnin Makurdi na jihar Binuwe.

Jami’in hukumar kiyaye hadurra ta kasa wato FRSC a jihar Binuwe, Aliyu Baba wanda ya samu zantawa da wakilin jaridar Daily Trust ta wayar salula ya shaida masa cewa mutum biyun da suka rasu namiji daya ne dan kabu-kabu da kuma matar da ya dauko kan babur din nasa.

KU KARANTA:Bamu da labarin sakin El-Zakzaky – IMN

Baba ya ce, hatsarin ya auku ne da misalin karfe 8:40 na safiyar Talata. Ya kara da cewa mutanen biyun da suka rasu sun sha wahala sosai ta yadda hukumar FRSC ma sai dai sha wuya kafin ta iya gano gawarwakin.

Ya kara da cewa: “ Mun samu gano sunan macen ta hanyar katinta na banki wato ATM wanda muka tsinta, yayin da shi kuwa namijin ba mu samu wani abu mai dauke da sunansa ba.

“ Mun samu damar ganin wayoyin mamatan na salula, kuma a yanzu haka maganar nan da nake maku wayoyin na hannun ‘yan sanda. Shi kuwa direban babbar motan da wannan abu ya rutsa da shi tuni ya riga ya kai kansa ofishin ‘yan sanda Division B Makurdi.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel