Harkar tsaro: Nauyin Gwamnatin Tarayya ya na hawa kan mu – Sakataren Gwamnatin Kaduna

Harkar tsaro: Nauyin Gwamnatin Tarayya ya na hawa kan mu – Sakataren Gwamnatin Kaduna

Gwamnonin jihohi sun bayyana cewa su na kashe kudin da ya kamata su yi amfani da su wajen gina makarantu da tituna da kuma asibitoci a taimakawa gwamnatin tarayya shawo kan tsaro.

Sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Malam Balarabe Lawal, da ya ke magana a madadin sauran Takwarorinsa na jihohin kasar, ya bayyana cewa ayyuka su na yi wa gwamnatocin jihohi yawa.

Balarabe Lawal ya yi wannan jawabi ne a lokacin da Sakataren gwamnatin tarayya watau Boss Mustapha ya kaddamar da wani kwamitin hadakar gwamnatoci jiya a babban birnin tarayya.

Malam Lawal ya ke cewa zai yi wa gwamntocin jihohi wahalar kula da hukumomi da ma’aikatun da ke karkashinsu. Lawal ya nemi gwamnatin tarayya ta rika kawowa jihohin na Najeriya dauki.

KU KARANTA: Akwai bashin Tiriliyan 1.2 a kan wasu Jihohin da ke da arzikin fetur

Sakataren na gwamnatin Kaduna ya na so gwamnatin tarayya ta rika ware wani kaso na kudin da ta ke da shi wajen dafawa gwamnoni ko kuma a kayyade iyakar ayyukan da jihohi za su rika yi.

Sakataren na Kaduna ya koka da cewa ba su samun isasshen lokaci da za su rika zama da SGF kamar yadda a ka shirya a makon nan.An yi wannan zama ne a Ranar 5 ga Watan Agustan, 2019.

A cewar Balarabe Lawal, gwamnoni na kashe makudan kudi wajen kula da matsalolin tsaro ta hanyar taimakawa ‘yan sanda, sojojin kasa da ruwa da jami’an hukumar NSCDC da dai sauransu.

Lawal ya ce ‘yan sanda kan nemi taimakon kusan komai a wajen gwamnoni don haka ya ji dadin yadda a ka kafa wannan kwamiti da zai rika duba alakar da ke tsakanin gwamnatocin kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel