Kungiyar Miyetti Allah ta shigar da gwamnatin jihar Benue kotu

Kungiyar Miyetti Allah ta shigar da gwamnatin jihar Benue kotu

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Horey, a ranar Litinin ta shigar da kara kotun daukaka kara domin kalubalantar shari'ar babban kotun Abuja na ranar 4 ga Yuli, 2019.

Kungiyar kare mutuncin Fulanin a karar da suka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/527/2017 ta hannun lauyoyinta, Aliyu Ahmed da Abdulhamid Mohammed, sun nuna rashin amincewarsu da hukuncin da alkali Okon Abang, ya yanke a watan jiya saboda haka suna bukatar kotu ta sake nazari a kai.

A bara, kungiyar Miyetti Allah ta shigar da kara kotu domin kalubalantar dokar hana kiwo a fili da majalisar dokokin jihar Benue tayi.

KU KARANTA: Kamar jihar Borno, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna ta kai ziyarar bazata asibiti

A ranar Asabar, 3 ga watan Agusta, gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta damke akalla makiyaya 81 kuma an kwace shanaye 3000.

Ortom wanda yayi mgana a bikin kungiyar yan kabilar Idoma mazauna Amurka, ya ce dabbaka dokan haramta kiwo a jihar ya kawo zaman lafiya jihar.

Yace:"Muna dabbaka dokarmu, kuma ana smaun zaman lafiya. A yau, mun damke makiyayya 81. An ci wasu tara kuma sauran na gidan yari."

"Mun samu cigaba. Duk inda muka ga shanaye suna kiwo a fili, zamu kamasu. Kawo yanzu mun damke shanaye 3000."

"Dokar ta zayyana cewa cikin kwanaki bakwai, mammalakan shanayen zasu biya tara kafin a mayar musu da dabbobinsu. Muna karban kudade a hannunsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel