Yanzu Yanzu: An rufe jami’ar ATBU bayan ruftawar gadar da ya kashe dalibai 4

Yanzu Yanzu: An rufe jami’ar ATBU bayan ruftawar gadar da ya kashe dalibai 4

Hukumar makarantar jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi ta ruffe makarantar na tsawo makonni biyu biyo bayan annobar ambaliyar ruwa da yayi sanadiyar mutuwar dalibanta.

Idan za ku tuna an tattaro cewa wasu adadin dalibai sun mutu yayinda wasu da dama suka jikkata lokacin da wata gada ta rufto sakamakon ambaliyar ruwa a yankin Gubi na Jami’ar.

Shugaban jami'ar, Abdulazeez Ahmed ya sanar da Channels TV cewa dalibai hudu ne suka mutu a annobar yayinda wasu takwas sun jikkata.

Hakazalika da yake tabbatar da lamarin, Shugaban dalibai na jami’ar, Naziru Mohammed ya bayyana cewa dalibai biyu ne kawai suka mutu yayinda wasu biyu suka jikkata.

A wani jawabi dauke da sa hannun Dr AG Hassan, Rijistaran jami’ar, ya umurci dalibai da su bar sansanin jami’ar ba tare da bata lokaci ba daga ranar 6 ga watan Agusta.

A cewar Mista Hassan, daliban za su dawo a ranar Litinin, 19 ga watan Agusta.

KU KARANTA KUMA: Zanga-zangar juyin hali: An zuba manyan jami’an tsaro a sabon wajen taron na Lagas

Shugaban jami’ar ya mika ta’aziyya da jaje ga iyaye, daliban makaranta da jami’ar baki daya akan wannan mummunan al’amari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel