Kamar jihar Borno, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna ta kai ziyarar bazata asibiti

Kamar jihar Borno, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna ta kai ziyarar bazata asibiti

Kamar yadda ya faru a jihar Borno da asuban yau, Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe, ta kai ziyarar bazata daya daga cikin manyan asibitocin jihar Kaduna dakr unguwar Rigasa a safiyar Talata, 6 ga watan Agusta, 2019.

Legit.ng ta samu wannan labari ne daga mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i inda ya bayyana yadda mataimakiyarsa ta samu likita daya kacal cikin likitoci biyar da ya kamata yace suna asibitin a lokacin.

Yayinda ya kammala ziyarar, ta bukaci shugaban likitocin ya ci tarar likitocin da suka ki zuwa aiki.

Jawabin yace: " Maigirma Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe da safiyan yau Talata ta kai ziyarar ba-zatta Babban Asibitin Gwamnati da ke Rigasa Kaduna inda ta taras da likita daya ne cikin manyan likitoci biyar da ke asibitin ya zo aiki.

Mataimakiyar Gwamnan ta umurci shugaban asibitin da ta ba sauran likitocin da ba a samu a aiki ba takardar amsa laifi, wato ‘query’ domin bayyana dalilinsu na rashin zuwa wurin aiki."

Kamar jihar Borno, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna ta kai ziyarar bazata asibiti

asibiti
Source: Twitter

Kamar jihar Borno, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna ta kai ziyarar bazata asibiti

Kamar jihar Borno
Source: Facebook

Kamar jihar Borno, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna ta kai ziyarar bazata asibiti

mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna ta kai ziyarar bazata asibiti
Source: Facebook

A bangare guda, Gwamnan jahar Borno, Frafesa Babagana Umara Zulum ya sake kai ziyarar ba zata wasu manyan asibitocin jahar Borno guda biyu dake garin Maiduguri,

Zulum ya kai wannan ziyara ne da asubancin Talata, da misalin karfe 5:40 indaya fara da babban asibitin zamani na Mohammed Shuwa, sa’annan daga bisani ya tsaya a ofishin ma’aikatan kiwon lafiya dake kan titin kasuwar Monday inda ake duba cututtukan fata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel