Bamu da labarin sakin El-Zakzaky – IMN

Bamu da labarin sakin El-Zakzaky – IMN

-Kungiyar IMN ta ce har yanzu ba a saki shugabanta ba daga hannun hukuma

-Wani babba a cikin kungiyar ta IMN ne ya bada wannan labarin inda yake cewa hukumar DSS dai ta samu takardar kotu mai bayani cewa an bai wa malam izinin tafiya Indiya

-Hukumar DSS ta ce tana cigaba ne da tuntunbar sauran hukuomin tsaro kafin sakin El-Zakzaky kamar yadda kotu ta bada umarni

Haramtacciyar Kungiyar Islamic Movement of Nigeria wato IMN, ta ce bata da labarin sakin Shugabanta Ibrahim El-Zakzaky daga hannun hukumar tsaron farin kaya ta DSS.

Da yake zantawa da jaridar Vanguard ranar Litinin, Shugaban kwamitin Free Zakzaky na IMN, Sheikh Abdulrahman Abubakar ya ce, abinda kawai kungiyar IMN ta sani shi ne takardun kotu sun isa hannun DSS.

KU KARANTA:EFCC: An samu dankara-dankaran motoci 21 a gidan Abdulaziz Yari

Da aka tambayesa kan mai zai ce game da labarin sakin El-Zakzaky sai ya ce: “ Ku bari na bincika tukuna. ‘Yan mintuna kadan da suka wuce hukumar DSS ta samu umarni daga kotu na cewa a sake shi. A halin yanzu hukumar na cigaba da tuntunbar hukumomin tsaro domin ganin an kammala duk wani shiri kan a sako malam. Zan iya ce maku har yanzu Zakzaky bai dawo garemu ba.

“ Idan kuma har akwai wani abu da zai taso zan sanar da ku saboda muna cigaba da bin diddigin al’amarin.”

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta amsa cewa tabbas za ta bi umarnin kotu wadda ta bada belin Ibrahim El-Zakzaky a bisa dalilin tafiya waje domin a duba lafiyarsa.

Wata babbar kotun jihar Kaduna ce ta bada belin malamin bayan ya nemi izinin tafiya kasar Indiya domin ganin likita.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar DSS, Dr Peter Afunanya ya tabbatar mana da wannan batun a wata hira da yayi da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Sai dai kuma har ila yau, hukumar DSS ba ta ce komi ba game da maidakin El-Zakzaky Zeenatu ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel