Zanga-zangar juyin hali: An zuba manyan jami’an tsaro a sabon wajen taron na Lagas

Zanga-zangar juyin hali: An zuba manyan jami’an tsaro a sabon wajen taron na Lagas

- Jami’an tsaro sun mamaye 'Freedom Park' a Legas da kewayenta

- Wajen shakatawan ya kasance harabar inda za a gudanar da zanga zangar juyin juya hali

- Babu masu zanga zangar ko magoya bayan zanga zangar a harabar wajen da sojoji suka karbe a halin yanzu

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun karbe harabar ‘Freedom Park’ wajen da aka shirya gudanar da zanga zangar juyin juya hali da aka sake shiryawa a Ojota da ke jihar Legas.

‘Freedom Park’ wajen shakatawa da aka sanya ma sunan marigayi Gani Fawehinmi, ya kasance wajen da masu zanga zangar kwato ma al’umma hakki a jihar ke yawan gudanar da zanga-zangarsu.

Sai dai jaridar This Day ta rahoto cewa akwai rundunar soji a mashigin wajen shakatawan.

An kuma tattaro cewa an tsaurara matakan tsaro a haraban yayin da masu zanga zanga basu hallaro ba ko.

KU KARANTA KUMA: Daga karshe: Yari yayi magana akan samammen da EFCC ta kai gidansa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a ranar Litinin, 5 ga watan Agusta, sojoji da yan sanda sun tarwatsa mambobin kungiyar da ke zanga-zangar juyin juya hali wadanda suka taru a babban filin wasa na kasa, a yankin Surulere da ke jihar Lagas.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa masu zanga-zangar wadanda suka isa filin wasan da misalin karfe 7:00 na safe domin fara zanga-zangar sun tarar da jami’an yan sanda a mashigin filin wasan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel