Yanzu-yanzu: Gada ya rufto wa daliban Jami'ar Bauchi, wasu da dama sun mutu

Yanzu-yanzu: Gada ya rufto wa daliban Jami'ar Bauchi, wasu da dama sun mutu

Dalibai da malamai na Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi suna cikin halin tashin hankali sakamakon rahotanni da ke nuna cewa wasu dalibai sun mutu sakamakon rufowa da wata gada tayi a jami'ar a daren Litinin.

Lamarin ya faru ne sakamakon ruwan sama mai karfi da akayi a jihar na tsawon awanni.

A halin yanzu ba tantance adadin wadanda suka mutu ba duba da cewa wasu majiya daga jami'ar sun ce ruwa ya tafi da mutane biyu yayin da wasu suka ce mutum uku ne wasu ma sun ce hudu.

DUBA WANNAN: Ganduje vs Abba Gida-Gida: PDP ce ta nemi a yi zaben kece raini - Yakasai

Daya daga cikin majiyar ta ce: "An fada min dalibai takwas sun mutu, wasu da dama kuma ba a gansu ba. An gano gawar daya daga cikinsu a sansanin sojojin sama da ke da nisar kilomita 5 daga jami'ar, wasu kuma ba a gansu ba."

A cewar wata majiya, "gadar da ta hada ajijuwa da dakunan kwanan dalibai ne ta rufto sakamakon ruwan sama da akayi a daren Litinin yayin da daliban ke komawa dakunnan kwanan su."

Wani dalibin jami'ar da ya nemi a sakayya sunansa ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 11.30 zuwa 12.00 na dare.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa daliban jami'ar suna rubuta jarrabawar su ta karshen zangon karatu na farko ne a halin yanzu.

Da aka tuntube shi a wayar tarho, Mai magana da yawun Jami'ar, Dr Andee Iheme ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa: "An kira taron gaggawa a safiyar yau kuma za mu kira taron manema labarai da zarar mun kammala taron."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel