Hajjin Bana: NAHCON ta kammala jigilar maniyyata 44,450 zuwa kasar Saudiya

Hajjin Bana: NAHCON ta kammala jigilar maniyyata 44,450 zuwa kasar Saudiya

Hukumar tabbatar da jin dadin Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta kammala jigilar manniyatan Najeriya 44,450 zuwa kasa mai tsarki. Wannan adadi ya hadar da ma'aikata da za su yi masu hidima daga dukkanin jihohin kasar da kuma garin Abuja.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayar da shaida, wannan adadi bai hadar da maniyyatan Najeriya ba wadanda suka dira a kasar Saudiya ta hanyar jirgin yawo.

Hukumomin kasar Saudiya sun yi wa Najeriya tanadin kujerun maniyyata 95,000 a bana. A yayin da jihohin Najeriya suka kasafta guraben kujerun maniyyata 65,000 karkashin kulawa ta hukumar jin dadin Alhazai, masu bibiyar jirgin yawo sun ribaci sauran kujerun 30,000.

NAHCON ta ce jirgi mai lamba Flynas XY5821, ya yi dakon sahun karshe na maniyyatan Najeriya 301 da kuma ma'aikata 19 bayan barin garin Abuja inda kuma ya isa filin jirgin saman birnin Jedda na kasar Saudiya da misalin karfe 8.53 na safiyar Litinin.

Jirgi cikon na 93 da ya yi jigila ta karshe a ranar Litinin, ya yi dakon maniyyatan Abuja, Sakkwato, Zamfara, Kaduna, Anambra, Abia, Kuros Riba, Delta, Ebonyi da kuma Enugu. Ya kasance jirgi da ya yi dakon rukunin karshe na maniyyatan Najeriya zuwa kasar Saudiya a bana.

KARANTA KUMA: Buhari ya saki Sowore cikin gaggawa - Secondus

Jihohi 32 na Najeriya da maniyyatansu suka daura haramar gudanar da aikin hajji a bana sun hadar da Filato, Jigawa, Borno, Legas, Bauchi, Taraba, Yobe, Oyo, Osun, Ogun, Gombe, Katsina, Kano, Kaduna, Nasarawa, Kebbi, Kwara, Kogi, Sakkwato, Adamawa, Neja, Edo, Ekiti, Ondo, Zamfara, Anambra, Abia, Kuros Riba, Delta, Ebonyi, Enugu da kuma birnin Tarayya Abuja.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel