Buhari ya saki Sowore cikin gaggawa - Secondus

Buhari ya saki Sowore cikin gaggawa - Secondus

Shugaba na babbar jam'iyyar hamayya ta kasa PDP, Prince Uche Secondus, ya kirayi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayar da umarnin gaggauta sakin Omoyele Sowore, jagoran masu akidar juyin juya-hali a Najeriya.

Secondus ya yi wannan kira a ranar Talata cikin birnin Yola yayin da ya kai wa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ziyara ta ta'aziyyar mahaifinsa, Umaru Badami da ya riga mu gidan gaskiya.

Cikin kalami nasa, Secondus ya ce, "ina kira ga shugaban kasa Buhari da ya saki Sowore cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba domin kuwa wannan al'amari ya nesanta gwamnatinsa daga dimokuradiya".

"Abubuwan da ke ci gaba da faruwa a kasar nan a halin yanzu sun zamto tamkar mun kasance a karkashin mulkin soji. Haka kuma gwamnati ta gaggauta sakin duk wani wanda ke tsare a sanadiyar akidarsa ta siyasa".

Sowore ya shiga hannun jami'an hukumar DSS a ranar Asabar da gabata biyo bayan kiran al'ummar kasa da su yi tururuwa wajen gudanar zanga-zangar bayyana kin jinin yadda al'amura suka tabarbare a kasar nan.

KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ta shafe gidaje 60, ta raba mutane 3,000 da muhallansu a Imo

Har wa yau kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito, Sowore yayin da yake tsare a hannun hukuma, ya ce a ci gab da gashi domin kuwa babu gudu babu ja da baya dangane da zanga-zangar nuna kin jinin mulkin danniya da gwamnatin Buhari ke yi a Najeriya.

Sowore wanda ya yi takarar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar AAC a yayin zaben kasa da aka gudanar a watan Fabarairu, ya bayyana matsayarsa a yayin da abokanan gwagwarmayarsa suka ziyarce shi a wurin da yake tsare.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel