Ambaliyar ruwa ta shafe gidaje 60, ta raba mutane 3,000 da muhallansu a Imo

Ambaliyar ruwa ta shafe gidaje 60, ta raba mutane 3,000 da muhallansu a Imo

Akalla mutane 3,000 sun rasa muhallansu a yayin a ranar Juma'ar da ta gabata ambaliyar ruwa ta hadidiye fiye da gidaje 66 a yankin Orsu Obodo na karamar hukumar Oguta dake jihar Imo. Wannan lamari ya uku a sanadiyar ruwan sama da aka yi ta shatatawa a 'yan kwanakin nan.

Ambaliyar ruwan ta auku biyo baya saukar ruwan sama tamkar da bakin kwarya na tsawon kwanaki uku. Wadanda suka rasa matsugunansu sun hadar da mata da kuma kananan yara kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayar da shaida.

Da yake gabatar da jawabai dangane da aukuwar wannan mummunan lamari, dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Oguta, Frank Ugboma, ya nemi gwamnati da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki da su kawo dauki na gaggawa domin saukaka radadin halin kaka-ni-kayi da mutanen Oguta suka tsinci kawunansu.

Dan majalisar ya mika kokon bararsa ga hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, da ta kwatanta jibintar lamarin da mutanen Oguta suka shiga wajen bayar da kayan agaji da zai rage masu radadin asarar da suka yi.

A daminar bara, annobar ambaliyar ruwa da kassara mutane da dama a Najeriya musamman jihar Katsina inda ruwa ya tafi da wata jaririya yayin da rayukan mutane fiye da arba'in suka salwanta a garin Jibiya.

Lamarin ya auku a sanadiyar yadda madatsar ruwa da kuma dam din garin na Jibiya suka cika suka tumbatsa sannan suka yi ambaliya a sanadiyar wani mamakon ruwa ruwan sama da aka shafe sa'o'i ana shatatawa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel