Zazzabin cizon sauro ya kashe mutane 1,800 a Burundi

Zazzabin cizon sauro ya kashe mutane 1,800 a Burundi

Cutar zazzabin cizon sauro ta salwantar da rayuka 1,800 na al'ummar kasar Burundi cikin wannan shekarar da muke ciki kamar yadda reshen jin kai da bayar da agaji na majalisar dinkin Duniya ya tabbatar.

Adadin rayukan da suka salwantar a sanadiyar bullar wannan annoba ya sanya tana gogayyar kafada da barkewar cutar Ebola a makociyar kasa ta Jamhuriyyar Congo.

Cikin wani sabon rahoto da reshen jin kai da bayar da agaji na majalisar dinkin Duniya ya fitar, ya bayyana cewa kimanin mutane miliyan 5.7 ne suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro wato Malaria a kasar Burundi cikin shekarar 2019 da muke cikinta.

A yayin da fiye da rabin adadin mutanen kasar Burundi suka kamu da cutar da cizon sauro ya haifar da ita, rayukann mutane 1,801 sun salwanta cikin kasar a tsakanin 1 ga watan Janairu zuwa 21 ga watan Yulin da ya gabata.

Reshen jin kai na majalisar dinkin Duniya, OCHA, yayin bayyana mamaki gami da damuwa, ya nemi dukkanin mahukunta masu ruwa da tsaki da su gaggauta bayar da gudunmuwa gwargwadon iko domin magance wannan annoba kafin ta kara ta'azzara.

Majalisar dinkin Duniya ta alakanta bullar wannan annoba a kasar Burundi da rashin amfani da gidajen sauro, sauye-sauyen yanayi, da kuma rashin wadatacciyar garkuwa ta kamuwa da zazzabin cizon sauro a tsakankanin al'umma.

KARANTA KUMA: Har yanzu Robert Mugabe na gadon asibiti tun watan Afrilu - Mnagagwa

An yi annobar cutar zazzabin cizon sauro cikin kasar Burundi a shekarar 2017 inda rayukan mutane 700 suka salwanta daga cikin mutane miliyan 1.8 da suka kamu da ita.

Kungiyar lafiya ta Duniya WHO, ta ce a shekarar 2017 da ta gabata, an samu bullar cututtuka daban-daban a kasashen Duniya yayin da kimanin rayukan mutane 435,000 suka salwanta cikin mutane fiye da miliyan 220 da suka kamu da rashin lafiya.

WHO ta ce kaso 90 cikin 100 na adadin wadanda suka kamu da kuma wadanda suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyar cutar zazzabin cizon sauro sun kasance 'yan Afirka.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel