Kaso 40% na yaran jihar Yobe ba sa zuwa makaranta

Kaso 40% na yaran jihar Yobe ba sa zuwa makaranta

Kwamitin kula da harkokin bunkasa ilimin makarantun firamare da na sakandire da gwamnatin jihar Yobe ta kafa ya tabbatar da cewa, akwai kimanin kaso 40 cikin 100 na yaran jihar da ba sa zuwa makaranta.

Jagoran kwamitin Farfesa Mala Daura, shi ne ya bayar da shaidar hakan a ranar Litinin cikin wata sanarwa yayin gabatar da sakamakon bincikensu ga gwamnan jihar Mai Mala Buni a fadarsa da ke birnin Damaturu.

Farfesa Daura yayin gabatar da sakamakon binciken kwamitin da ya jagoranta, ya alakanta tabarbarewa harkokin ilimi a jihar da rashin samun gudunmuwar cibiyoyin gargajiya a jihar.

Kazalika ya alakanta wannan koma baya da ta'azzarar ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram da ya mamaye yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ya kuma ce kaso 30 cikin 100 na malaman makarantu a jihar ba su da cikakkiyar cancantar karantarwa da hakan ya yi tasiri wajen haifar da rashin nasarar dalibai a jarabawar kammala karatun sakandire.

KARANTA KUMA: Har yanzu Robert Mugabe na gadon asibiti tun watan Afrilu - Mnagagwa

Kwamitin ya kuma gargadi gwamna Buni da ya gaggauta tantance dukkanin malamai da kuma ma'aikata da ke makarantu a fadin jihar domin tabbatar da macancanta.

Gwamna Buni ya yabawa kwazon kwamitin tare da shan alwashin ribatar shawarwarin da suka gabatar nan ba jimawa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel