Gwamnan jahar Borno ya kai ziyarar ba zata asibitoci da Asubah

Gwamnan jahar Borno ya kai ziyarar ba zata asibitoci da Asubah

Gwamnan jahar Borno, Frafesa Babagana Umara Zulum ya sake kai ziyarar ba zata wasu manyan asibitocin jahar Borno guda biyu dake garin Maiduguri, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Gwamna Zulum ya kai wannan ziyara ne da asubancin Talata, da misalin karfe 5:40 indaya fara da babban asibitin zamani na Mohammed Shuwa, sa’annan daga bisani ya tsaya a ofishin ma’aikatan kiwon lafiya dake kan titin kasuwar Monday inda ake duba cututtukan fata.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya yi ma yan wasa ruwan daloli a jahar Kano

Gwamnan jahar Borno ya kai ziyarar ba zata asibitoci da Asubah

Zulum
Source: Facebook

Da yake zagayensa, gwamnan ya bayyana damuwarsa game da halin daya tsinci asibitin fatan, wanda yace yana bukatar kulawa na musamman, a yanzu haka ya bada umarnin a fara aiki a cibiyar domin gyaranshi.

Daga karshe Gwamna Zulum ya tabbatar da cewa zai cigaba da zagaya bangarori daban daban na gwamnatin jahar Borno tabbatar kowa na aikinsa yadda ya kamata.

Gwamnan jahar Borno ya kai ziyarar ba zata asibitoci da Asubah

Zulum
Source: Facebook

A wani labarin kuma, gwamnan ya dakatar da shugaban likitocin babban asibitin zamani na Umar Shehu da wasu kananan likitoci guda hudu, wadanda ya tarar basu je wurin aikinsu ba yayin wata ziyarar gani da ido daya kai asibitin a makon jiya.

Gwamnan ya yi kokarin kiran likitocin ta wayar tarho yayin da bai tarar dasu a wajen aikin ba, amma dukkansu babu wanda ya dauki wayansa, kamar yadda kaakakin gwamnan Isah Gusau ya bayyana.

“An dakatar da Dakta Musa Chuwang da Dakta Chijoke Ibemere da suka kaurace ma zuwa aiki, yayin da aka dakatar da Dakta Baba Ali Malgwi wanda bai dauki kiran da gwamna ya yi masa ba, duk da cewa yana zama a rukunin gidajen cikin asibitin. Ita ma Dakta Esther an sallameta.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel