Wani mutumi ya kashe abokinsa da ya fadi gasar karo-da-karo na rago bayan ya sa N500

Wani mutumi ya kashe abokinsa da ya fadi gasar karo-da-karo na rago bayan ya sa N500

Jami’an yan sanda sun kama wani mutum mai suna Segun, kan zargin chaka ma abokinsa, Yusuf, wanda ya fadi gasar fadar raguna, wuka har lahira a yakin Isawo da ke Ikorodu, jihar Lagas.

An tattaro cewa sabani ya shiga tsakanin abokan bayan Segun ya lashe gasar N500 da ya sanya ma ragonsa a ranar Lahadi.

An rahoto cewa Yusuf ya far ma Segun da wani fasasshen kwalba.

Wani mazaunin yankin, Kizito Isibor, yace Segun ya chaki Yusuf da wuka a kokarinsa na kare kansa, wanda yayi sanadiyar mutuwarsa.

Ya bayyana cewa: “Lamarin ya afku a hanyar Tapa a yankin Oke Oko da ke Isawo a Ikorodu da musalin karfe 11:00 na safiyar ranar Lahadi. Yusuf da Segun na zama a unguwa guda sannan kuma sun kasance abokan juna.

“Segun ya sanya gasar N500 akan ragonsa domin su kara da ragon wani mutumi sannan ragonsa yayi nasara. Daga bisani sai musu ya kaaure a tsakanin Segun da Yusuf. Dukkansu biyun suka kama dambe sannan mutanen da ke wajen suka shiga lamarin.

“Sai daga bisani suka yanke shawarar komawa wani waje domin ci gaba da fadan. A hanyarsu na zuwa wajen, sai Yusuf ya naushi Segun sannan yayi kokarin chaka masa kwalba, amma a kokarinsa na kare kansa, sai Segun ya fito da wuka ya soki Yusuf a kirji.”

KU KARANTA KUMA: Annabin karya da ya fito daga kasar Amurka ya mutu, kwanaki kadan bayan ya kai ziyara kasar Kenya

Isibor yace an kama Segun sannan aka mika shi hannun yan sanda, yayinda aka kai gawar Yusuf ofishin yan sanda.

Kakakin yan sandan jihar, ala Elkana, yace marigayin ya sanya gasa akan ragon da ya fadi, inda ya kara da cewa an tura lamarin zuwwa ga sashin kisan kai na jihar domin bincike, da Panti, Yaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel