EFCC ta na facaka da dukiyar al’umma a Kotu a kai na, alhali ban da laifi- Adoke

EFCC ta na facaka da dukiyar al’umma a Kotu a kai na, alhali ban da laifi- Adoke

Mohammed Bello Adoke, wanda ya rike mukamin Ministan shari’a kuma Lauyan gwamnati a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fito ya na mai wanke kansa.

Mohammed Bello Adoke ya zargi hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa da laifin kitsa masa sharri tare da kashe dukiyar al’umma wajen bincikensa a gaban kotu.

Bello Adoke ya karyata zargin da ke kansa a game da badakalar da a ka samu wajen cinikin rijiyar man OPL245. Adole ya yi wannan jawabi ne a farkon makon nan domin maida martani ga EFCC.

Adoke ya karyata cewa ya tsere daga shari’ar da a ke yi a kan rijiyar man Malabu inda ya ce babu hannunsa a laifin da a ke zarginsa da su. Tsohon Ministan ya ba EFCC shawara da ta janye karar da ta kai.

Babban Lauyan ya ce ganin irin bayanai masu tona asiri da kamfanonin Shell da ENI su ke yi a kotu inda a ke shari’a a kasar Italiya, ya kamata hukumar EFCC ta rufawa kanta asiri ta janye karar da ta shigar.

Wani Jakadan kasar Rasha da a ke bincike, Ednan Tofik ogly Agaev, ya bayyanawa kotu cewa ya ambaci sunan Bello Adoke ne a cikin wadanda su ka ci kudin rijiyar Malabu adalilin tursasa masa da a ka yi.

KU KARANTA: Akwai masu yaudarar mutane da suna na – Inji Gwamnan Imo

Jim kadan bayan wannan bayani da Ednan Tofik Agaev ya yi ne kuma tsohon shugaban kamfanin ENI, Vincenzo Armanna, ya tabbatar da haka. Tsohon Ministan ya ce wadannan jawabai sun wankesa.

A cewar Adoke, babu kanshin gaskiya a zargin da EFCC ta ke yi masa na cewa ya ci amanar kujerarsa a lokacin ya na Minista wajen cinikin OPL 245 da kamfanin Shell da ENI wanda yanzu magana ta kai kotu.

Tsohon Ministan ya ce ba a lokacin Goodluck Jonathan a ka saida wannan rijiyar mai ba, abin ya faru ne tun sa’i’lin da Sani Abacha ya ke mulki, sai kuma Olusegun Obasanjo ya karbe rijiyar da ya zama shugaban kasa.

Mista Adoke ya ce shawara kurum ya ba gwamnatin Jonathan cewa ta bi abin da kotu ta ce a game da shari’ar da a ka yi a kan wannan rijiyar mai. Adoke ya ce sam babu sunansa cikin wanda su ka ci kudin rijiyar.

A game da batun cewa ya tsere zuwa Turai, Ministan ya bayyana cewa tun kafin a fara wannan bincike ya tafi jami’ar Leiden ta kasar Holland domin ya karo ilmi. Ya ce wasu ne ke amfani da Ibrahim Magu a kansa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel