Tubabbun yan bindiga sun bayyana dalilin da yasa suka fara daukan makamai

Tubabbun yan bindiga sun bayyana dalilin da yasa suka fara daukan makamai

Wasu tubabbun yan bindiga a karamar hukumar Tsafe ta jahar Zamfara sun bayyana abin da yasa suka fara daukan makamai, suna satar mutane tare da garkuwa dasu da kuma kai hare hare a kauyuka.

Yan bindigan sun bayyana haka ne yayin wani taron sulhu daya gudana a fadan sarkin tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa a ranar Litinin, 5 ga watan Agusta, inda suka ce cin mutuncin da yansanda da yan sakai suke musu ne ya tunzurasu ga daukan makamai.

KU KARANTA: Karamar yarinya yar shekara 10 ta haihu a jahar Benuwe

Guda daga cikin yan bindigan, Hassan Dantawaye ya fede biri har wutsiya a yayin zaman inda yace: “Tunzuramu aka yi zuwa daukan makamai, saboda baya ga cewa an sace mana shanunmu, sai kuma jami’an tsaro da yan sakai suka fara zaluntarmu.

“Babu damar mu shiga kasuwa sai su kamamu, a duk inda suka yaranmu zasu tafi makaranta ko matanmu, sai su kama su kashe, mu kanmu sai mun biya makudan kudade kafin Yansanda su sakemu, a wasu lokuta ma jami’an tsaro sun kai mana hari suna kashemu ba tare da laifin komai ba.

“Don haka bamu da wata mafita illa mu dauki makamai mu fara satar mutane, muna garkuwa dasu da kuma aikata wasu munana laifuka.” Inji shi.

Shima wani shugaban al’ummar Fulani, Alhaji Madele ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jahar Zamfara data samar da wannan zaman sulhu, inda ya roketa ta karesu daga kungiyoyin yan sakai da kuma jami’an tsaro dake kai musu hari babu gaira babu dalili.

Daga karshe kwamandojin yan bindigan sun yi alkawarin sako dukkanin mutanen da suka yi garkuwa dasu. Suma shugaban yan sakai na jahar Zamfara, Alhaji Yahaya Ahmad ya tabbatar da goyon bayansu ga sulhun da gwamnati ke yi da yan bindigan.

“Daga yau ba zamu sake kai ma Fulani makiyaya hari ba, kuma zamu bi umarnin gwamnati game da haka, Fulani zasu iya yawonsu a garin Tsafe da sauran garuruwanmu ba tare da tsoro ko tsangwama ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel