Hukumar AMCON ta karbe kamfanin Bao Yao Huan Jian da ke Najeriya

Hukumar AMCON ta karbe kamfanin Bao Yao Huan Jian da ke Najeriya

Mun ji cewa babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ya hukumar AMCON mai kula da kadarorin Najeriya dama ta karbe wani kamfani da a ke tunani tsohon gwamnan jihar Benuwai ya mallaka.

A wata shari’a da a ka yi, Alkali Binta Nyako ta bayyana cewa AMCON ta na da hurumin da za ta maida kamfanin karafunan nan na Bao Yao Futurlex Iron & Steel Company Limited karkashinta.

Haka zalika kotun ta ba hukumar damar karbe kamfanin Bao Yao Futurlex Iron & Steel Company Limited da ke Najeriya. Shen Yaozhang da kuma Idris Garba su ne su ka mallaki kamfanin.

Shen Yaozhang mutumin kasar waje ne yayin da shi kuma Idris Garba ya taba yin gwamna a jihar Benuwai a lokacin mulkin soji. Kotu ta kuma bada izni a rufe asusun bankin wannan kamfani.

KU KARANTA: AMCON za ta sa kafar wando daya da masu cin bashi su gagara biya

Hukumar ta AMCON ta bayyana wannan a wani jawabi da ta fitar Ranar Lahadi, 4 ga Watan Agusta, 2019, a game da wannan hukuncin da Alkali mai shari’ar yanke a makon da ya gabata.

Nyako ta kuma ba AMCON damar karbe filin wannan kamfani da ke cikin Kauyen Esuk Utan da ke Garin Kalaba a jihar Kuros Riba. Kotu ta kuma nemi a garkame duka asusun wannan kamfani.

Bayan nan kuma akwai wani fili da ke layin Idoma close a cikin Garin Kaduna na Bao Yau Han da ya koma hannun gwamnatin tarayya. A na bin su bashin Biliyan 3.6 ne wanda a ka gagara biya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel