Ba zan daina magana a kan cin zalin da Buhari ke yi ba - Atiku

Ba zan daina magana a kan cin zalin da Buhari ke yi ba - Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai cigaba da magana a kan kama karya da cin zalin fararen hula da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ke yi.

A wani jawabi da Paul Ibe, kakakin Atiku, ya fitar, dan takarar shgaban kasar a jam'iyyar PDP ya ce gwamnatin Buhari ba ta iya yin abinda ya dace a lokacin da ya dace sai ya yi magana.

Atiku ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin Najeriya tayi burus da batun rahoton kungiyar UNDP da ya bayyana cewa 'yan Najeriya miliyan 98 na rayuwa a cikin kungurmin talauci saboda bai ce uffan a kan batun ba.

"A ranar 10 ga watan Yuli majalisar dinkin duniya ta zaburar da gwamnatin Najeriya a kan yadda gwamnatin Buhari ta lalata tattalin arzikin Najeriya tare da jefa mutane miliyan 98 cikin mummunan talauci.

DUBA WANNAN: Har ila yau: Hukumar DSS ta kama tsohon editan jaridar Daily Trust

"Amma kamar yadda suka saba, Buhari da mukarabban gwamnatinsa basu ce komai ba a kan alkaluman da UNDP ta fitar dangane da tsanantar talauci a tsakanin 'yan Najeriya.

"Watakila, har yanzu sun ki yin magana a kan lamarin ne saboda gaskiya ce aka fito da ita, wacce bata yi musu dadi ba.

"Daya dalilin da zai sa gwamnatin har yanzu ta ki yin magana shine saboda Atiku bai yi magana a kan rahoton ba," a cewar jawabin.

Jawabin ya kare da cewa matukar sai Atiku ya yi magana kafin gwamnati ta dauki matakin da ya dace, Atiku ba zai taba rufe bakinsa yana gani ana cin zalin 'yan Najeriya da yi musu kama karya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel