'Yan bindiga sun kwace miliyoyin kudi a hannun akawun gwamnatin jihar Niger

'Yan bindiga sun kwace miliyoyin kudi a hannun akawun gwamnatin jihar Niger

‘Yan bindiga hudu sun kai ma babban akawu na ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Niger hari, sannan suka saci kudi sama da naira miliyan 9.5.

Lamarin ya gurgunta harkokin tattalin arziki a garin Minna har na tsawon sa’o’i biyu, yayinda matafiya da masu motoci suka nemi hanyoyin tserewa.

An tattaro cewa babban akawun, Idris Abdullahi na a hanyarsa na dawowa daga wani bankin cikin garin Minna inda ya ciro kudaden da misalin karfe 10:30 na safe.

An gano cewa kudin ya kasance na gudanar da wasu ayyuka a offishin shugaban ma’aikatan.

Wani idon shaida ya fada ma manema labarai cewa yan bindigan sun tsare motar akawun ne a lokacin da yake kokarin shiga harabar Sakateriyar, inda suka yi harbi a iska sannan suka dauke kudin dake motarsa sannan suka tsere.

Majiyin har ila yau yace yan bindigan sun bi hanyar ofishin kwastam da ke hanyar western bye-pass inda motarsu ta samu matsala, wanda hakan yayi sanadiyan barin motan.

Har ila yau sun kwace wata mota wacce ta taimaka musu wajen tserewa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Daga karshe DSS ta saki El-Zakzaky bayan umurnin kotu

An yi kokarin tuntubar ofishin Shugaban Ma’aikata don samun bayanai akan lamarin amman ba ayi nasara ba a lokacin hada wannan rahoton.

A lokacin da aka tuntubi kakakin yan sandan jihar, Mohammad Abubakar, ya tabbatar da aukuwan lamarin, inda ya ce jami’an tsaro suna nan suna bin diddigin yan fashin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel