Har ila yau: Hukumar DSS ta kama tsohon editan jaridar Daily Trust

Har ila yau: Hukumar DSS ta kama tsohon editan jaridar Daily Trust

Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama tsohon editan jariar Daily Trust, Ibrahim Dan-Halilu, bisa zarginsa da goyon bayan harkokin kungiyar na da ta shirya gudanar da zanga-zangar juyin juya hali a Najeriya.

A ranar Asabar ne jami'an hukumar DSS suka yi awon gaba da Omoyele Sowore, shugaban kungiyar da ta shirya gudanar da zanga-zangar, a dakin Otal dinsa a jihar Legas.

Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa jami'an hukumar DSS, a cikin wasu kananan motoci hudu, sun dira a gidan Dan-Halilu da ke unguwar Rigachikun a jihar Kaduna da misalin karfe 2:00 na safiyar ranar Litinin tare da yin awon gaba da shi.

Rabi'atu, matar Dan-Halilu, ta shaida wa Daily Nigerian cewa jami'an na DSS sun fara karbe wayoyinsu tare da yi musu binciken kwakwaf kafin daga bisani su yi awon gaba da mijin nata shi kadai.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun tarwatsa wadanda suka fito zanga-zangar juyin hali (Hotuna)

"Sun bayyana mana cewa su jami'an DSS ne, sun karbi waya ta tare da umarta ta na biyo su zuwa dakinmu inda suka kira lambarsa daga waya ta.

"Da suka ga sunan da ya bayyana a waya ta sai suka tambaye ni ina mai wayar, sai na fada musu cewa ai lambar mijina ce.

"Shine suka umarce shi ya shirya ya biyo su zuwa ofishinsu," a cewar Rabi'atu.

Sai dai, da aka tuntubi kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, domin karin bayani bai amsa kira ba kuma bai dawo da sakon da jaridar Daily Nigerian ta aika masa ba.

Wani bincike da jaridar ta gudanar ya nuna cewa Dan-Halilu ya bayyana goyon bayansa ga zanga-zangar juyin juya hali a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel