Sauke nauyin da rataya a wuyanmu ya sanya muka kai simame gidan tsohon gwamna Yari - EFCC

Sauke nauyin da rataya a wuyanmu ya sanya muka kai simame gidan tsohon gwamna Yari - EFCC

Hukumar EFCC mai yaki da rashawa a Najeriya ta bayyana cewa sauke nauyin da rataya wuyanta na hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ya sanya ta kai simame gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari.

Mai magana da yawun hukumar, Mista Tony Orilade, shi ne ya bayar da tabbacin hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin cikin birnin Abuja.

Jami'an hukumar EFCC sun kai simame gidan tsohon gwamnan Zamfara a daren Lahadin da ta gabata.

Orilade ya ce bincike da hukumar ke ci gaba da gudanarwa ya sanya suka kai simame gidan tsohon shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya da ke karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara.

Jami'in hukumar ya ce babu wata manufa ta kai simame gidan tsohon gwamnan illa iyaka ci gaba da gudanar da bincike domin sauke nauyin hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati da ya rataya a wuyanta.

KARANTA KUMA: Harry Maguire da 'yan wasan baya 4 mafi tsada a duniya

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, wannan shi ne karo na biyu da hukumar EFCC ta gudanar da bincike a gidan wani mashahurin mutum bayan saukarsa daga kujerar mulki a wannan shekarar ta 2019 da muke ciki.

Hukumar EFCC ta kai makamancin wannan simame gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha.

A watan Dasumban 2018 ne hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kebbi, Usman Sa'idu Dakingari, a gaban kotu bisa zargin halasta kudin haramun.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel