An yanke hukuncin zaman shekar 5 a kurkuku ga wani Fasto da ya yi ma yarinya fyade

An yanke hukuncin zaman shekar 5 a kurkuku ga wani Fasto da ya yi ma yarinya fyade

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Ado-Ekiti ta sanar da yanke hukuncin shekara 5 a gidan kurkuku ga wani limamin coci, Gabriel Asateru mai shekaru 56 bayan kamashi da laifin yi ma wata yarinya yar shekara 5 fyade.

Lauyan mai shigar da kara, Ronke Odefola ta shaida ma kotu cewa Fasto Asateru ya aikata laifin nearanar 23 ga watan Disambar 2016 a wani gida dake titin Ayebaju, a unguwar Ifisin na jahar Ekiti, inji rahoton jaridar Guardian.

KU KARANTA: Tanimu Akawu ya musanta zargin Hadiza Gabon da Maryma Yahaya da karuwanci

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Limamin, wanda Fasto ne a cocin Anglican ya yi ma wata karamar fyade ne a lokacin da ya kai ma iyayenta ziyara, kuma tun a watan Janairu na shekarar 2018 aka fara shari’ar, sai dai Limamin cocin ya musanta tuhumar.

Amma da yake bangare masu shigar da kara sun shirya da hujjojinsu, sun gabatar ma kotu shaidu guda uku kwarara, wanda suka tabbatar ma kotu laifin da Limamin cocin ya aikata, haka zalika an gabatar da rahoton likitoci da suka duba yarinyar, da kuma jawabin wanda ake kara daya rubuta a caji ofis.

Da wannan ne Alkalin kotun, Oluwatoyin Abodunde ta tabbatar da gamsuwar kotu da duk bayanan da bangaren masu shigar da kara suka gabatar a gabanta, don haka ta yanke ma Fasto Asateru hukuncin shekara 5 a gidan Kurkuku.

Haka zalika Alkali Abodunde ta umarceshi ya biya taran N50,000, kamar yadda kundin dokokin kare hakkin kananan yara na shekarar 2006 ta tanadar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel