Aliko Dangote, Lawan, Wase, Sufetan ‘Yan Sanda, sun halarci bikin Fatima Sule a Akwanga

Aliko Dangote, Lawan, Wase, Sufetan ‘Yan Sanda, sun halarci bikin Fatima Sule a Akwanga

Mun ji cewa manyan kasa da dama sun halarci daurin auren ‘Diyar gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda a ka yi a cikin Garin Nasarawa a Ranar Asabar 6 ga Watan Agusta, 2019.

Kamar yadda mu ka samu rahoto, an daura auren Fatima Abdullahi Sule da Angonta Abdulhakeem Sunmonu ne a fadar Mahaifin gwamnan na Nasarawa watau Sarkin Gudi Alhaji Sule Bawa a Garin Akwanga.

Babban Limamin Masallacin Gudi, Sheikh Muhammad Surajo, ya yi wa Ango da Amarya addu’a bayan ya daura auren. An kuma biya N100, 000 ne a matsayin sadaki kamar yadda addinin musulunci ya koyar.

KU KARANTA: Barawo ya yi gaba da agon Miliyoyi na wani Sanata a Najeriya

Mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, shi ne ya zama Waliyyin Amarya. Shi kuma Usaman Sunmonu,ya tsaya a matsaya Wakilin Angon. Aliko Dangote shi ne wanda ya bada auren wannan Yarinya a ranar.

Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan; da kuma mataimakin shugaban majalisar wakilan Najeriya, Ahmed Idris Wase sun halarci wannan daurin aure. Haka zalika IGP Mohammed Adamu ya samu zuwa.

Tsofaffin gwamnoni kuma Sanatoci a yanzu irin su Kashim Shettima da Umaru Almakura na jihar sun halarci biki. An kuma hangi gwamnan jihar Filato Samuel Lalong da Babagana Zulum na Borno a wajen.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel