Barawo ya zare ma wani Sanata agoguna 3 da kudinsu ya kai N13,140,000

Barawo ya zare ma wani Sanata agoguna 3 da kudinsu ya kai N13,140,000

Dubun wani gogaggen barawo ta cika bayan ya yi awon gaba da jakar wani tsohon Sanatan Najeriya, Sanata Ifeanyi Araraume daga cikin jirgin sama, sa’annan ya kwashe masa wasu manyan agoguna masu tsada.

Legit.ng ta ruwaito lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Agusta yayin da Sanatan tare da matarsa suka sauka daga jirgin fasinja na Air Peace a filin sauka da tashin jirage na Sam Mbakwe dake jahar Imo.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta kai farmaki gidan tsohon gwamnan Zamfara Abdul Aziz Yari

Sai dai saukarsa ke da wuya sai ya nemi jakarsa ya rasa, don haka ya kama gabansa, suka yi tafiyarsu zuwa gida da matar tasa. Amma cikin ikon Allah yayin da wata daga cikin fasinjojin da suka shiga jirgin ta isa gidan masaukin baki na Rock View Hotel, sai ta ci karo da wani mutumi dauke da jakar.

Daga nan wannan mata ta tunkari wannan mutumi, wanda ta bayyanashi a matsayin babban mutum, ta tuhumeshi cewa ta gane wannan jakar dake hannunsa, kuma jakan kawunta ne, nan da nan ta kira Yansanda.

Zuwan Yansanda keda wuya suka kama mutumin, sa’annan suka amshe jakar, amma koda suka bude jakar ashe tuni mutumin ya kwashe wasu agoguna manya guda 3, wanda kowannensu kudinsa ya kai $12,000, a jimlace dai kimanin N13,140,000.

A wani labarin kuma, hukumar yaki da rashawa da makamantan laifuka, ICPC, ta kwato wasu kayayyaki da darajarsu ta kai N117,123,375.44 daga hannun tsohon Sanata mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Utazi Chukwuka.

Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai Keke Napep guda 51, babura 168, injin nika 203 da na’urar rarraba wutar lantarki 5 wanda aka bankadosu a cikin wani gida dake garin Mkpologu cikin karamar hukumar Uzo-Nwani ta jahar Enugu, mallakin Sanatan.

ICPC ta bankado wannan almudahana ne a kokarin da take yi na tabbatar da kowanne Sanata da dan majalisa ya gudanar da ayyukan da yayi alkawarin gudanar ma jama’ansa, kuma ya sanya a cikin kasafin kudi, wanda ake kira ‘Constituency project’ a turance.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel