NNPC ta bayyana dalilin karin kudin farashin Kalanzir

NNPC ta bayyana dalilin karin kudin farashin Kalanzir

Kamfanin dillan man fetur na kasa (NNPC) ya lakanta tashin farashin kalanzirin girki a fadin kasa da yawan buktarsa da ake yi 'yan kwanakin nan.

Mista Ndu Ughamadu, shugaban sashen hulda da jama'a na NNPC, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Abuja cewa an sabunta farashin kalanzir.

"Abinda nake son na bayyana shine an sabunta farashin kalanzir.

"Farshin Kalanzir na hawa da sauka ne saboda ba a saka matakai masu yawa a kansa kamar Fetur ba.

"Akwai karuwar bukatar Kalanzir, kuma hakan ne ya jawo tashin farashinsa. Matukar bukatar kalanzir ta karu, farashinsa zai karu a cikin gida," a cewarsa.

A cewar Ughamadu, NNPC ce kadai ke shigo da Kalanzir duk da matatun Fetur na cikin gida na samar da shi.

Ya bayyana cewa NNPC za ta tabbatar da cewa akwai isashen Kalanzir da zai wadaci bukatar 'yan Najeriya.

"NNPC na yin iya bakin kokarinta domin tabbatar da cewa akwai wadatuwar Kalanzir a cikin kasa, musamman saboda kasancewarsa sinadarin da talaka wa suka dogara da shi domin amfani a cikin gidajensu wajen yin abubuwa da dama," a cewar Ughamadu.

Wani bincike da NAN ta gudanar a unguwannin gefen birnin tarayya, Abuja, irinsu Kubawa, Dutsen Alhaji da Zuba, ta gano cewa gidaen mai da dama basa sayar da Kalanzir kwata-kwata.

Ana samun Kalanzir a kasuwar bayan fage a kan farashin N400 zuw N500 kowacce lita a Abuja.

Halima Saidu, wata mata da ke sayar da Kalanzir a kasuwar Kubwa, ta shaida wa NAN cewa babu tsayayyen farashin Kalanzir a gidajen man fetur.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel